21 Mayu 2026 - 00:33
Source: ABNA24
Fashe-Fashe Masu Ƙarfi A Ma'aikatar Tsaron Siriya

Majiyoyin cikin gida a Siriya sun ba da rahoton jin karar fashewa a yankunan Duwaila da Bab Tuma a Damascus, babban birnin Siriya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Wannan fashewar ta faru ne kusa da daya daga cikin gine-ginen da ke da alaƙa da ma'aikatar tsaro ta gwamnatin "Jaulani". Majiyoyin cikin gida sun ce bayan fashewar, ana ci gaba da jin karar harbe-harbe.

Majiyoyin cikin gida sun kara da cewa wannan fashewar ta faru ne a ofishin kayan aiki na ma'aikatar tsaro ta Siriya.

Wasu majiyoyi sun ce wannan fashewa sakamakon bam ne da aka kera a cikin gida.

.............

Your Comment

You are replying to: .
captcha